31 Agusta 2026 - 17:59
Source: ABNA24
Iran Ta Lalata Kayan Aikin Soji Da Wuraren Da Jiragen Yakin Makiya Suke Ajiye + Bidiyo

Rundunar Tsaro ta Juyin Juya Halin Musulunci ta sanar da cewa: An lalatar da kayan aikin fasaha da gyare-gyare da kuma wuraren da jiragen yakin makiya suke ajaiye a sansanonin sojan saman Amurka guda biyu na Malik Hussein da Al-Azraq.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Sojojin ta'addanci na Amurka a yammacin ranar Lahadi, 30 Ogusta 2026, sun sake keta 'yancin kasa da 'yancin kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda suka kai hari a wasu sassan tsibirin Lark, wanda ya haifar da shahada da raunata wasu masu kare ƙasa da 'yan'uwanmu masoya, da kuma barnar dukiyoyin jama'a da fafaren hula.

Rundunar Tsaro ta Juyin Juya Halin Musulunci da sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a matsayin mayar da martani ga wannan cin zarafin makiya, nan take suka mayar da martani mai tsanani ga makiya Amurka da sahyoniyya ta hanyar tsara wannan aiki.

Rundunar Tsaro ta Juyin Juya Halin Musulunci a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa: Ta lalata kayan aikin fasaha da gyare-gyare da kuma wuraren da jiragen yakin makiya suke tsugunna a sansanonin sojan sama na Amurka guda biyu na Malik Hussein da Al-Azraq.

'Yan mintoci da suka wuce, mayaƙan jarumtaka na rundunar sararin samaniya ta IRGC, a matsayin mayar da martani ga harin sama na makiya Amurka da sahyoniyya a tsibirin Lark, a cikin wani aiki na hukunta masu cin zarafi, na hadin gwiwa na makamai masu linzami da jirage marasa matuki da taken "Ya Muhammad ibn Abdullah (SAW)", sun lalatar da kayan aikin fasaha da gyare-gyare da kuma wuraren da jiragen yakin makiya suke ajiye a sansanonin sojan sama na Amurka guda biyu na Malik Hussein da Al-Azraq a Jordan, tare da harba makamai masu linzami na ballistic, kuma sun yi musu barna mai yawa.

Ofishin Hulɗa Da Jama'a Na Rundunar Tsaro Ta Juyin Juya Halin Musulunci

……………………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha